Type Here to Get Search Results !

An damke yansanda da suka bindige budurwa har lahira

Wasu ‘yan sanda biyu na tsare bayan sun yin harbin da yayi sanadiyar mutuwar wata budurwa ‘yar shekara 17.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas Hakeem Odumosu ya ce ana binciken jami”an masu mukamin ASP da Isfekta domin gurfanar da su.

Da yake ta’aziya ga iyalan marigayiyar kwamishinan ya bukaci jama’a su kwantar da hankali domin ana ci gaba da tsare mutanen.

Kakakin Rundunar DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa Kwamishinan ya umarci a zurfafa binciken musababbin kisan Tina Ezekwe.

“Yan sandan da ake zargi da yin harbin na tsare ana ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu

“Sun hadar da ASP Theophilus Otobo da Isfekto Oguntoba Olamigoke masu aiki a caji ofis din Bariga.

“A ranar 26 ga watan Mayun 2020 a yankin Berger Yanaworu  wadanda ake zargin suka yi harbi.

“Ya jikkata wani Musa Yakubu, harsashi ya sami budurwar a cinya ya yi sanadiyar mutuwar ta,” in ji shi.

DSP Bala Elkana ya ce ba a san dalilin harbin ba. An kai budurwar asibiti amma ta mutu bayan kwana biyu.

“Rundunar na takaicin lamarin, muna kuma ci gaba da tuntubar iyalin marigayiyar.

“Jama’a su kwantar da hankali domin muna yin duk abun da ya kamata a kan lamarin,” inji shi.

Yace rundunar zata ci gaba da sanar da al’umma halin da ake ciki game da lamarin.

Rahotun Aminiya


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN