Osinbajo ya bayyana ma Buhari muhimman hanyoyi 2 da zai bi don inganta rayuwar yan Najeriya

Rahotun Legit
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shawarci gwamnatin Najeriya ta bayar da kulawa kyauta ga yan Najeriya marasa lafiya dake asibiti ba tare da biyan sisi ba.
Daily Trust ta ruwaito hakan na cikin shawarwarin da hukumar sayar da kadarorin gwamnati da Osinbajo yake jagoranta ta baiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Osinbajo ya shawarci Buhari ya baiwa marasa lafiya kulawa kyauta, kuma ya inganta wutar lantarki a Najeriya, wadannan abubuwa biyu za su matukar amfanar miliyoyin yan Najeriya.
A ranar Talata ne hukumar ta amince da shawarwarin, wanda zasu bayyana su ga shugaban kasa Buhari, tare da kudurin dokar kwaskwarima ga bangaren kiwon lafiya, bada jimawa ba.
Cikin wani sako da kakaakin Osinbajo ya wallafa a shafin Twitter, Laolu Akande, yace daga cikin manyan batutuwan da majalisar ta tattauna akwai batun wuta da kiwon lafiya.
“Gyaran da gwamnatin Buhari za ta yi zai tabbatar da miliyoyin yan Najeriya da ba su iya biyan kudin asibiti sun samu kyakkyawar kulawa kyauta daga wajen gwamnati da zarar an kaddamar da sabon tsari.” Inji shi.
Mambobin hukumar sun hada da Osinbajo, zababbun ministoci, gwamnan babban bankin Najeriya da kuma shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnatin.
A wani labari kuma, saboda rashin kudaden shiga da hukuma kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya, FAAN, ke fama da shi, ta ce ba za ta ta iya biyan cikakken albashin ma’aikata ba.
Hukumar ta bayyana cewa ma’aikata za su fuskanci canji a albashinsu daga watan Mayu, amma da zarar jirage sun cigaba da tashi za ta cigaba da biyansu cikakkun hakkokinsu.
Hukumar FAAN ta shiga matsalar albashi ne tun bayan da aka dakatar da sauka da tashin jirage a Najeriya a wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus tun a watan Afrilu.
Rashin zirga zirgan jiragen yasa aka samu nakasu a kudaden shigar hukumar, don haka a ranar 19 ga watan Mayu ta sanar da ma’aikatanta halin da ake ciki.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN