Rahotun Legit
Allah ya yi wa mai bawa Gwamna Muhammadu Badaru shawara na musamman akan harkokin ilimin manya da na manyan makarantu, Ibrahim Ismail, rasuwa.
Marigayi Jarman Ringim kuma tsohon shugaban hukumar cigaban kananan hukumomi ya rasu ne a ranar Jumaa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin babban mataimaki na musamman ga maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a sabbin kafafan sadarwa, Auwalu D. Sankara a shafinsa na Facebook.
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya yi ta’aziyya ga daukacin al’ummar da ke masarautar Ringim bisa rasuwar Alhaji Ibrahim Ismail Jarman Ringim wanda ya rasu ranar Jumaa bayan fama da rashin lafiya da ya yi.
Alhaji Badaru da karshe yayi addua ga Allah subhanahu wata’ala da ya saka wa mamacin da aljanna firdausi kuma ya bai wa iyalan sa karfin gwiwar juriya da rashin da su kayi.
Gwamnan wanda ya misalta mamacin a matsayin mutum mai kamala da tausayin al’umma wanda yake fifita bukatun al’umma fiye da na sa.
Harzuwa lokaci da ya rasu, Ibrahim Ismail ya kasance na kusa da gwamna Badaru, inda yake da matsayi na mai bawa gwamna shawara akan harkokin ilimin manya da na manyan makarantu inda a kwanakin ya zama shugaba harkokin cigaban kananan hukumomi.
A wani labarin daban, kun ji cewa kotun tafi da gidanka a jihar Kano na hukunta wadanda suka saba dokar kulle da aka kafa sakamakon bullar COVID-19 ta zartar da hukunci a kan wasu limamai biyu da aka samu da laifin saba dokar.
An yanke wa limaman biyu hukuncin share gidan hakimi har na tsawon kwanaki bakwai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Baba Jibo Ibrahim, Cif Rajistara na jihar Kano ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumaa 9 ga watan Mayu.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a karamar hukumar Minjibir na jihar.
Kotun ta yanke hukuncin cewa limamen su rika share gidan hakimin Minjibir na tsawon sati daya baya da tarar Naira 10,000.
Ya kara da cewa a lokacin da suke gudanar da wannan aikin, jamian karamar hukumar za su rika zuwa suna duba su domin tabbatar da cewa sun aikata aikin yadda ya dace.
DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Tags:
ZURU