Inna lillahi: Yadda mutum dari suka mutu cikin mako daya a Bauchi

Rahotun Legit
A kalla mutane 100 ne suka mutu a garin Azare da ke jihar Bauchi a makon da ta gabata inda suka yi fama da rashin lafiya mai alamomi da ke kama da na masu ciwon coronavirus.
Azare ne gari mafi girma a jihar bayan Bauchi, babban birnin jihar
Ibrahim Mohammed Baba, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltan Katagum ne ya bayyana hakan cikin wata wasikar neman taimako da ya aike wa Shugaba Muhammadu Buhari kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.
Baba ya ce mace macen da ake zargin COVID-19 ce ta yi sanadi ya jefa alummar garin cikin tashin hankali da damuwa.

Tsohon dan majalisar ya ce kusancin garin na Azare da Bauchi, Kano da wasu manyan garuruwa a Jigawa ya saka ta cikin hatsarin kamuwa da cutar.
Ya ce, "Kusancin Azare da Bauchi, Kano da wasu manyan birane a Jigawa ya saka alummar garin cikin hatsarin kamuwa da cutar duba da cewa ta yadu a sauran garuruwan.
"Saboda haka, ina kira ga shugaban kasa ya umurci Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, da kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 su kai wa Azare dauki cikin gaggawa.
"Kazalika, ina son tunatar da kai cewa akwai sashin kula da ciwon ido da dakin gwaji da Bankin Kasa ta gina a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare tun 2013 amma ba a kaddamar da shi ba har yanzu.
"Ana iya fara amfani da shi a sauya shi zuwa cibiyar killace da yi wa masu COVID-19 magani a kuma sayo kayayyakin da ake bukata kamar su Ventalator.
"Duba da cewa wannan harka ce ta rai, ina fata saboda kishin kasa da kaunar kiyaye lafiyar yan Najeriya za ka taimaka wa mutanen Azare da kewaye a magance wannan matsalar."
Idan ba a manta ba, tsohon Alkali, Justice Dahiru Saleh wanda ya yanke hukuncin soke zaben Juna 12 a 1993 ya mutu a ranar Alhamis a Azare.
Rahotanni sun ce coronavirus ce ta yi sanadin rasuwarsa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN