Matar da dansanda ya harba a ciki da bindiga don saba dokar hana zirga zirga ta mutu

Wata mata mai shekara  35 da ke zaune a babban Kasuwar Jinja a kasar Uganda ta mutu sakamakon raunukan harbin bindiga da ake zargin wani dansanda a motar sintiri ya harbe ta a ciki bisa zargin ta saba dokar hana zirga zirga sakamakon cutar Korona.

Matar mai suna Evelyn Namulondo ta mutu ne ranar Juma'a da safe bayan an garzaya Asibitin da ita tun ranar Laraba da lamarin ya faru.

Shugaba Nyoweroi Musaveni ya sa dokar hana zirga zirga daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6.30 na safe. Namulondo mai sayar da abince ne a Kasuwar Jinja, sakamakon haka ta je domin ta sayi yayan itace da take girki da su da karfe biyar bayan ta abar gidanta ada ake Mazabar Budhumbuli , amma sai dansanda ya harbeta da bindiga a ciki.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN