Yansandan jihar Imo sun kama wani saurayi dan shekara 23 mai suna Uchenna Mbahotu bayan an yi zargin cewa ya keta budurcin wasu yara kanana ya da kanwa.
Bayanai sun ce saurayin na zaune a gida daya ne da iyayen yaran suna haya, kuma an yarda da shi bisa amanan zamantakewa, amma ya yi amfani da wannan dama ya ci amanar uwayen yaran ta hanyar yin lalata da su.
Yaran yan shekara 9 da 11 ne kuma yan gida daya ya da kanwa.
Kakakin yansandan jihar Imo Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce za a gurfanar da wanda ake zargi da zarar yansanda sun kammala bincike.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari