Wasu yansanda a jihar Niger sun tsinci jaririya sabuwar haihuwa a bola nadev a cikin laida a birnin Minna kuma suka dauke ta a cikin boot na motarsu suka kai ta Asibiti.
Wani Likita da ke bakin aiki lokacin da yansandan suka kawo jaririyar ya wallafa a shafinsa na Twitter yadda yansandan suka shigo da wannan jaririya Asibiti a cikin yanayi na ban tausayi.
Ya ce bayan yansandan sun ji kukan jariri a cikin bola, da yake an dade ana sheka ruwan sama, sai suka tsaya suka duba kuma suka ga cewa ashe jaririya ce aka jefar a bola. Sakamakon haka suka dauko jaririyar suka kai ta Asibiti inda Dr Bright Oris ya ceto rayuwar jaririyar bayan jikinta ya dauki tsananin sanyi sakamakon dukan ruwan sama da aka yi mata a bola.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari