• Labaran yau


  Sallah: Batun kar a duba wata labarin karya ne, jama'a su fita duban wata - Imam Muhktar

  Limamin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi Imam Abdullahi Muhktar (Walin Gwandu) ya ce labaran karya ne ake yadawa cewa kada a duba Wata ranar 29 ga watan Ramadan.

  Imam Muhktar ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan kammala Sallar Juma'a da ya jagoranta a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi a garin Birnin kebbi ranar 22 ga watan Mayu wanda ya zo daidai da ranar 29 ga watan Raamadan.

  Limamin ya bukaci al'umma Musulmi su fita domin dubin Wata kamar yadda aka saba a kowane 29 ga watan Ramadan. Ya yi kira ga Kwamitin duban Wata cewa su fita gangaren Barikin yansandan kwantar da tarzoma da ke yammacin garun Birnin kebbi domin duban wata da Magariba.

  Hakazalika an sanar cewa duk wanda ya ga wata a wajen garin Birnin kebbi da kewaye,  ya hanzarta sanar da Uban kasa na garinsu, Kwamitin duban wata, ko Fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sallah: Batun kar a duba wata labarin karya ne, jama'a su fita duban wata - Imam Muhktar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama