• Labaran yau


  Dokar hana zirga zirga: Kotu ta kama Sheikh Rigachukun ta ci shi tarar N5000 a Kaduna

  An kama Malamin ne a  Shataletalen Jami'ar jihar Kaduna (KASU) domin bai sa takunkumin fuska ba tare da danshi. Ya bayar da uzurin cewa kafar sadarwar Kaduna State edia Corporations ce ta gayyace shi domin ya gabatar da wani shirin Rediyo.

  Aisha Dikko ta ce " An tuhumi Rigacukun tare da danshi da laifin rashin sa takunkumi kuma aka ci su tarar N5000 kowanensu".

  Ta kara da cewa Kotun tafi da gidanka ta kuma umarci Malamain ya gabatar da wani shiri da zai fadakar da jama'a hanyoyi da jama'a za su bi domin su kare yaduwar cutar Korona"

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dokar hana zirga zirga: Kotu ta kama Sheikh Rigachukun ta ci shi tarar N5000 a Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama