• Labaran yau


  Jami'in LATSMA ya suma bayan dansanda ya yi masa duka da kulki a bakin aiki

  Wani jami'in LATSMA mai suna Roland Fuludu ya suma bayan ya sha dan karen duka daga wajen wani jami'in dansanda mai suna SP Femi a Apapa da ke birnin Lagos .

  Dansandan yana aiki ne a shiyar aikin dansanda na Zine 13 a birnin na Ikko.

  Diyar Roland ta ce mahaifinta ya gaji da tursasawa da SP Femi ke yi masa, domin yana karya dokokin hanya da bayar da cin hanci. Sakamakon haka mahaifinta ya gaji kuma ya ki. Daga bisani Femi yayi masa dan banzan duka da kulkin yansanda lamari da ya kaishi ga suma.

  An garzaya zuwa Asibiti da Roland, bayan ya farfado ya labarta yadda lamarin ya faru.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jami'in LATSMA ya suma bayan dansanda ya yi masa duka da kulki a bakin aiki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama