Type Here to Get Search Results !

Gwamnatin Jigawa ta ce Almajirai 28 sun kamu da cutar Korona a jihar

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce Almajirai guda 28 sun kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito. Hakan ya kawo adadin almajiran da suka kamu da kwayar cutar ta COVID-19 zuwa 31 a Jigawa cikin kwanaki biyu da suka gabata. A ranar 13 ga watan Mayun 2020,

Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC ta tabbatar da mutum 141 da suka kamu da cutar a jihar. Abba Zakari, Kwamishinan Lafiya na jihar wanda shine kuma shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar korona ta jihar Jigawa ya tabbatar da sabbin wadanda suka kamu da cutar a ranar Alhamis a Dutse.

A cewarsa, hakan ya kawo jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar yanzu 169, cikin su uku sun mutu. "A ranar Laraba, NCDC ta fitar da alkaluman sabbin wadanda suka kamu da cutar kuma ka san muna aiki ne da dakin gwaji a Kaduna don yi wa almajiran da aka dawo mana da su Jigawa gwaji," a cewar Kwamishinan.

"Baya ga sabbin mutum 23 da suka kamu, mun kuma samu wasu karin almajirai 28 da suka kamu da cutar. "A cikin 23 da NCDC ta sanar, uku daga cikinsu almajirai ne, hakan ya kawo jimillar 51. Kuma cikin 51, 31 daga ciki almajirai ne." Ya kara da cewa nan da kwanaki ka dan, gwamnatin jihar za ta kafa sabuwar dakin gwaji a babban asibitin Dutse da ke babban birnin jihar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN