Duba dalili da ya sa Buhari baya saka takunkumi domin kariya kan cutar Korona

Mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari kan harkar Soshiyal Mediya  Lauretta Onochie ta ce shugaba Buhari baya saka takunkumin rufe baki da hanci ne domin yana cikin yanayi nagartacce.

Hukumar NCDC, ma'aikatan lafiya na tarayya da sauran sashen kula da lafiyan al'umma sun sha sanarwa tare da bukatar jama'a su dinga amfani da takunkumi domin zama kariya ga cutar Korona.

Sai dai sau da yawa ake ganin shugaba Buhari yana gudanar da taruka a Fadar shugaban kasa, amma an kula shi kadai ne baya sanye da takunkumi.

Lauretta ta ce dokar shi ne, wadanda ke shigowa zuwa wajen ganin Buhari su ne ake bukatar su saka takunkumi, domin su ne ke shigowa, amma yanayi fadarshugabn kasa ingantacce ne.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN