• Labaran yau


  Dattijo mai dauke da coronavirus a jihar Kebbi da ya gudu kafin a killace shi ya mutu a gida

  Mutum na biyu da ake zargin yana dauke da cutar coronavirus da ya tsere kafin a killace shi ya rasu a gida a jihar Kebbi.

  Kwamishinan lafiya na jihar Kebbi Alhaji Jaafaru Muhammed ne ya shaida wa manema labarai haka a Birnin kebbi ranar Asabar.

  Ya ce mamacin dan shekara sittin ne wanda ke fama da cutar suga da hawan jini, kuma ya kara da cewa yan uwanshi ne suka kawo shi FMC Birnin kebbi daga UDUTH Sokoto kafin a tura shi wajen da ake kula da matsalar cutar coronavirus.

  Ya ce an dauki gwaji daga wajen mutumin ranar 25 ga watan Aprilu, amma sai ya gudu kafin a kai shi wajen da ake killace wadanda ake zargin kamuwa da cutar coronavirus. Sai dai dattijon ya mutu a gida ranar 26 ga watan Aprilu.

  Ko da sakamakon gwajinsa ya fito ranar 29 ga watan Aprilu, ya tabbatar cewa dattijon ya kamu da cutar coronavirus kafin ya mutu.

  Sakamakon haka jami'ai suka shiga neman wadanda dattijon ya yi mu'amala da su kafin rasuwarsa, domin daukan matakai da suka dace.

  Yan kwamitin kula da cutar sun gano mutum 12 da dattijon ya yi mu'amalan kurkusa da su da kuma karin wasu mutum 17 da ya yi hulda da su.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dattijo mai dauke da coronavirus a jihar Kebbi da ya gudu kafin a killace shi ya mutu a gida Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama