Allah ya yi wa Ministan ayyuka da kwadago na Jamhuriyar Nijar Muhamed Ben Omar rasuwa.
Guardian ta ruwaito cewa an sanar da rasuwar Ministan ne ranar Lahadi a birnin Niamey, hakazalika jam'iyarsa ta Social Democratic Party ta tabbatar da rasuwarsa.
Duk da yake ba a fadi musabbabin rasuwarsa ba, amma jama'a na zargin ko mutuwarsa na da nasaba da cutar coronavirus.
Jamhumriyar Nijar na da mutum 736 da ke dauke da cutar COVID-19 yayin da mutum 35 suka mutu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari