Duba yadda ake sabon kiran sallah a Najeriya sakamakon cutar coronavirus

Rahotun BBC Hausa

Sakamakon hana sallar jam'i da hukumomi a kasashen duniya daban-daban suka yi don kiyaye lafiyar jama'a daga cutar korona, yanzu masu kiran salla wato ladanai, na amfani da salon kiran salla na lokacin annoba. 

Maimakon yadda aka saba inda ladan kan yi kira ga jama'a su hallara domin a yi sallar jam'i, yanzu ladanai kan yi amfani da wasu kalamai ne na daban - na bukatar jama'a su yi salla a gidajensu.

Wannan wani salon kiran salla ne da mutane da dama ba su taba ji ba sai a wannan lokaci na annobar Korona.

Zakariyya Muhammad - babban ladani na babban masallaci na kasa da ke Abujar Najeriya - ya shaida wa BBC cewa yanzu idan an kira sallah cewa ake mutane su yi sallah a gidajensu.

"Yanzu idan mun kira sallah sai mu ce ala sallu fi rihalikum ko kuma fi biyutikum wato ku yi sallah a gidajenku," in ji Zakariyya.

Mallam Muhammad Zakariyya ya ce shi kansa bai taba jin irin wannan kiran sallar ba a rayuwarsa kuma bai taba yi ba a tsawon shekara 27 da ya yi yana ladanci.

"Ba mu taba ji ba sai a irin wannan lokaci na korona, mun dai karanta a litattafai cewa ana yin irin wannan kiran salla," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Wannan kiran salla ya samo asali ne a lokacin manzon Allah a yanayi irin wannan, lokacin da aka yi ruwa mai ban mamaki.

"Sai manzon Allah ya umarci sahabbansa da su fada wa mutane cewa su yi sallah a inda suke ko kuma gidaensu.

"Shi ne mu ma yanzu muke yi. Maimakon mu ce hayya alassalati hayya alalfalahi, sai mu ce sallu fi biyutikum ko sallu fi rihalikum."

Mallam Zakariyya ya koka game da yadda ake kiran sallah amma sai masallaci ya kasance fayau.
"Abin babu dadi - a kira sallah amma sai ka ga masallaci ba kowa ko kuma ka ga mutane kowa ya ja gefe yana sallah shi kadai."

Addinai a fadin duniya sun shiga wannan bakon halin ne tun daga watan Fabarairu - lokacin da cutar korona ta fara fantsama kasashen duniya - inda aka saka dokar hana fita a akasarin kasashen
Cutar ta faro ne daga birnin Wuhan da ke yankin Hubie na kasar China a watan Disambar 2019. A ranar 11 ga watan Maris Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cutar a matsayin annoba ta duniya.

Ya zuwa yanzu, annobar korona ta halaka mutum kusan 250,000 a fadin duniya, yayin da kusan miliyan uku da rabi suka kamu, a cewar alkaluman Jami'ar Johns Hopkins.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN