Rahotun BBC Hausa
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce cutar korona ta yi ajalin wani dan majalisar jiha Hon Sule Adamu.
Gwamnan
jihar Abdullahi Sule ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar ga manema
labarai yayin da yake bayani kan halin da ake ciki kan annobar korona.
Mai
taimakawa gwamman kan harakokin watsa labarai ya shaida wa BBC cewa dan
majalisa ya nuna alamun cutar korona kuma ya rasu ne kafin fitar da
sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar.
Gwajin kuma ya tabbatar da yana dauke da cutar.
Yanzu gwamnatin ta rufe zauren majalisar jihar tare da killace dukkanin 'yan majalisar don dakile bazuwar cutar a jihar.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari