Covid-19: Fusatattun matasa sun yi wa Alkalan Kotun tafi da gidanka duka a Taraba

Rahotun Legit


Akalan kotun tafi da gidanka da ke hukunta direbobin da suka karya dokar hana zirga-zirga a jihar Taraba sun sha dukan tsiya a hannun wasu fusatattun matasa a ranar Litinin.

Fusatattun matasan sun katse aikin kotun yayin da take zamanta a yankin karamar hukumar Gassol da ke kan babbar hanyar Wukari zuwa Jalingo, sannan sun zane alkalan kotun, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta ce da kyar alkalan suka samu suka gudu zuwa cikin wata gonar rake da ke kusa da wurin domin tsira daga matasan.

A cewar Daily Trust, hatta tsirarun jami'an rundunar 'yan sanda da takwarorinsu na NSCDC da ke gadin kotun sai guduwa suka yi saboda ba zasu iya dakatar da fusatattun matasan ba. Matasan sun lalata dukkan takardu da sauran kayan aikin kotun tare da yin awon gaba da 'yan kudaden da aka ci tarar direbobi.

Wani shaidar gani da ido ya sanar da Daily Trust cewa, "kawai ganin fusatattun matasan mu ka yi kamar daga sama, kuma basu wani bata lokaci ba wajen fara dukan alkalan kotun." Daily Trust ta ce bincikenta ya gano cewar yanzu haka jami'an rundunar 'yan sanda sun fara farautar matasan wadannan matasa domin gurfanar da su.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin. "An samu matsala da wasu fusatattun matasa a Tella, wadanda suka katse zaman kotun tafi da gidanka duk da yanzu an shawo kan lamarin," a cewarsa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN