Bidiyon yadda askarawan saman Najeriya suka dagargaza ma'adanan makaman boko haram

Legit Hausa

Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wa wani yanki da mayakan Boko Haram ke amfani da shi hari. Dakarun sun yi wa yankin Parisu da ke dajin Sambisa a jihar Borno ruwan wuta ta sama, jaridar The Nation ta gano hakan.

Wannan harin da dakarun suka kai ya tarwatsa wurin ajiyar makaman mayakan Boko Haram din. An yi nasarar halaka wasu daga cikin 'yan ta'addan kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa. Kamar yadda takardar da ta fito daga shugaban fannin yada labarai na hukumar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce sun kai harin ne bayan bayanan sirrin da suka samu a kan 'yan ta'addan.

Kamar yadda takardar ta bayyana: "A cikin kokarin tabbatar da zaman lafiya da ts aro a yankin arewa maso gabas na kasar nan, rundunar sojin saman Najeriya ta ragargaza wasu 'yan ta;adda da kuma makamansu. "Al'amarin ya faru ne a yankin Parisu da ke dajin Sambisa na jihar Borno. 'Yan ta'adda da yawa sun rasa ransu a harin ranar 30 ga watan Afirilun 2020."

Kamar yadda yace, "An kai harin ne bayan samun bayanan sirri daga majiya mai karfi a kan harkokin 'yan ta'addan da yankin da suke." Kamar yadda aka hango ta jiragen sama na yakin, an ga yankin da 'yan ta;addan suke kwana da kuma wuraren ajiye makamansu.

"Rundunar sojin saman Najeriyan za ta ci gaba da kokarin ganin bayan makiyan kasar nan har sai zaman lafiya ya tabbata a dukkan sassan kasar nan," yace. A wani labari na daban, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta ce dakin gwajin coronavirus na biyu a jihar Kano ya kammala.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta shafinta na twitter a ranar Alhamis. Hukumar ta ce dakin gwajin na nan a jami'ar Bayero da ke Kano. "Dakin gwaji na 18 a kasar nan ya kammala a jami'ar Bayero da ke Kano. Shine na biyu a jihar. "Mun mayar da hankali wajen samar da dakunan gwajin cutar kamar yadda dabarun gwaji suka bayyana," wallafar tace.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN