• Labaran yau


  An yi ram da mutane da aka boye tsakanin dabbobi a cikin mota domin shiga dasu Kaduna

  An kama wasu bayin Allah da aka boye su a cikin dabbobi a motocin Trela guda biyu domin shiga da su garin Kaduna daga jihar Kano ranar Alhamis.

  Kwamishinan tsaron jihar Kaduna da ayyukan musamman Samuel Aruwan ya ce an kama wadannan mutane ne bayan an sami labarin sirri.

  Ya kara da cewa an kama mutanen ne a kan iyakan boda tsakanin jihar Kano da Kaduna, domin har sun zarce zuwa garin Gwargwaji a karamar hukumar Zaria na jihar Kaduna.

  Ya ce  wadanda aka gano an boye su ne  tsakanin dabbobi, babura da sauran kayakin da aka dauko a cikin motocin.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An yi ram da mutane da aka boye tsakanin dabbobi a cikin mota domin shiga dasu Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama