• Labaran yau


  Ba zamu lamunta da kashe mutane da sunan ramuwar gayya ba - Buhari

  Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tur da matakin kashe kashen bayin Allah da sunan ramuwar gayya sakamakon tashin hankali tsakanin Fulani da Addara a jihar Kaduna.

  Buhari ya ce ba daidai bane Fulani da Addarawa su dinga kashe junansu ta hanyar kai hari da ramuwar gayya ga junansu a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.

  Ya ce daukan matakin taimaka wa kai marmakin amfani da doka shi ne dalili da ya ke jawo fadadar kashe kashen.

  Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai ba Buhari shawara kan harkar Labarai Garba Shehu, wanda ya ce shugaba Buhari ya yi gargadin cewa ba wanda ke da hurumin daukan doka a hannunsa.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ba zamu lamunta da kashe mutane da sunan ramuwar gayya ba - Buhari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama