• Labaran yau


  Gurnanin majalisar dokokin jihar Kebbi ya sa Gwamnati ta saki N2.4b don biyan yan fansho

  Jama'an jihar Kebbi musamman wadanda Gwamnati jihar Kebbi ke rike da Gratutinsu suna ci gaba to da  yin ruwan albarka ga Majalisar Dokokin jihar Kebbi bisa gurnani mai karfin gaske da ta yi ga Gwamnati da Majalisar zartarwar jihar Kebbi domin ganin an biya yan Fansho da Gratuti hakkinsu a fadin jihar,

  A wani yanayi da ya ba jama'an jihar Kebbi mamaki, ganin cewa fiye da shekara biyar tun hawansu kujearar wakilcin jama'an jihar Kebbi, Majalisa bata taba fitowa ta fuskanci Gwamnati ko Majalisar zartarwar jihar Kebbi karara bisa hakkokin jama'a kamar yadda ta yi a wannan karo ba ka musamman kan hakkin yan Fansho da jama'ar jihar Kebbi.

  Lamari da masu fashin baki kan lamurran siyasan jihar Kebbi ke nuni da cewa Majalisar dokokin jihar Kebbi ta yi "Gurnani mai karfi da ya razana mahukunta kuma ya aika babban sako ga masu ruwa da tsaki wajen sha'anin mulkin jihar Kebbi". Wanda masana lamaurran siyasa suka ce hakan ya ja wa Majalisar martaba a idanun jama'an jihar Kebbi

  Kasa da mako daya bayan Majalisan dokokin ta bukaci Gwamnatin jihar Kebbi ta biya yan Fansho da Gratuti hakkokinsu, lamari da tun hawan wannan Gwamnati kan mulkin jihar Kebbi ake ta kai kawo da yan Fansho da Gratuti kan a biya su hakkokinsu, amma sai gashi kalma daya daga Majalisar dokokin jihar Kebbi ya canja akalan lamurra a shugabance da kuma siyasance.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gurnanin majalisar dokokin jihar Kebbi ya sa Gwamnati ta saki N2.4b don biyan yan fansho Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama