An kama yan acaba 29 makare a cikin babban mota a Abuja, duba dalili

Kwamitin kula da matsalar Korona a birnin tarayya Abuja, ta kama yan Acaba 29 makare a cikin wata babban mota da suka taso daga Lafia na jihar Nassarawa kan hanyarsu ta zuwa Lagos ranar Talata.

An tsayar da mmotar ne mai lamba LFA 837 ZX a kan gadar AYA da ke gundumar Asokoro

Direban motar mai suna Samaila Samiya, ya ce ya yanke shawarar daukar yan Acaban ne bayan sun roke shi, kuma suka ce za su bashi N2000 kowannensu domin ya kaisu Lagos daga garin Lafia.

Daya daga cikin fasinjan mai suna Musa Simon,ya ce su yan Acaba ne da suka baro garin Lagos bayan bullar cutar Korona, ya kara da cewa masu baburan sun yi barazanar cewa za su sayar da baburan matukar yan Acaban basu ci gaba da aikin nemo kudi da su ba. Sakamakon haka suka yanke shawarar cewa su koma Lagos domin neman abin rufin asiri.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari