Allah Ya yi wa Sarkin Ban Bichi a jihar Kano Doktar Wada Ibrahim Waziri rasuwa a safiyar yau Laraba 27 ga Mayu, 2020.
Marigayi Wada Waziri ya bar duniya yana da shekaru 89, bayan fama da rashin lafiya mai nasaba da yawan shekaru.
Da yake mika ta’aziyya ga iyalen mamacin, Gwamnan Jihar Kano ya bayyana marigayin a matsayin babban jigo a sarautar Kano.
Sanarwar ta’aziyyar ta bayyana rasuwar a matsayin gagarumar rashi ga jihar Kano, masarauta da fagen siyasa.
A lokacin kuruciyarsa Marigayi Wada IbrahimWaziri ya yi aiki a matsayin ma’aikacin jinya. Sarakin tsohon ma’aikacin gwamnati ne kuma dan siyasa.
Wasu sarautun daya rike a baya sun hada da Sa’in Kano, Hakimin Makoda da Dambatta. Marigayin shi ne Sa’in Bichi kuma Hakimin Dambatta.
Rahotun Aminiya
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI