Saboda mangoro matashi ya kashe danuwansa, kalli hotunan yadda lamarin ya faru

Rundunar yansandan jihar Abia ta tabbatar da kama wani saurayi mai suna Chinedu Omeonu bayan ya kashe danuwansa mai suna Solomon Monday Orji a Mgboko Umuoria da ke karamar hukumar Obingwa a jihar Abia.

Rahotanni sun ce dan gidan Orji ya je gidan Kawunsa Chinedu domin ya tsinci Mangoro da suka fado daga bishiya.

Sai Omeonu ya far wa dan gidan Orji da duka har yaron ya suma, daga bisani  Orji ya je gidan Kawunsa ya tambaya ko wane laifi yaron ya yi da aka yi masa duka har ya suma.

Cikin tsananin fushi Omeonu ya dauko Adda ya sassare Orji, lamari da ya sa ya mutu, sai Omeonu ya yi kokarin tsrewa, amma matasa suka kama shi suka lafta masa dan banzan duka kafi su mika shi ga jami'an yansanda.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN