• Labaran yau


  Yawan mutane da suka kamu da coronavirus a Duniya sun zarce miliyan daya - Bincike

  Fiye da mutum  1,002,159 ne suka kamu da cutar coronavirus a fadin Dimiya kamar yadda sakamakon bincike na wasu masu nazari da bincike kan cutar a Jami'ar John Hopkins suka gudanar .

  Kididdigan wadanda suka mutu sakamakon cutar ya zarce 51,000, yayin da mutum 208,000 suka warke

  Kasar Italia ce ke da yawan adadin wadanda suka mutu na mutum  13,915, yayin da kasar Spain ke bi mata da yawan wadanda suka mutu guda 10,003.


  Kasar Amurka na da yawan wadanda suka kamu da cutar mutum  234,000 yayin da 5,316 suka mutu kawo yanzu.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yawan mutane da suka kamu da coronavirus a Duniya sun zarce miliyan daya - Bincike Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama