Dokar coronavirus: Duba yadda aka sami takaddama tsakanin soji da yansanda a Abuja

Rahotun Legit Hausa


Yayin da jami’an tsaro suke aikin dabbaka dokar ta baci da gwamnatin tarayya ta sanya a garin Abuja, Legas da Ogun, an samu takaddama a tsakanin wasu dakarun Sojin Najeriya da jami’an Yansanda a unguwar Nyanya na Abuja.

 Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da wasu hafsoshin rundunar Sojan sama guda biyu suka tuka mota ba’a kan hanyarsu ba, har Yansanda suka tare su.

Tare su ke da wuya sai Yansandan suka nemi su koma baya, su je su bi hanyar da ta kamata, amma Sojojin suka kekashe kasa suka nuna taurin kai tare da dagewa a kan lallai ba zasu koma ba, sai dai Yansandan su basu hanya su wuce. Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa:

“Nan take Sojojin suka shiga zagi tare da cin mutuncin Yansandan, har da kwamandansu mai suna Azeez Idowu.” Wannan ne Yasa Yansanda suka yi kokarin kama Sojojin biyu. Ana cikin wannan takaddama sai kuma ga wasu tawagar Sojojin sama nan sun iso wurin da ake rikicin da nufin kwatar abokan aikinsu ko ta halin kaka, amma Yansandan suka atafau ba zasu kyale su ba.

A nan ma aka cigaba da cacar baki wanda hakan ya janyo zaman dar dar a yankin, da kyar aka shawo kan lamarin bayan wani babban hafsan Sojan sama ya nuna rashin gaskiyar Sojojin, sa’annan ya uamrce su su baiwa Yansandan hakuri.

A wani labarin kuma, babban daraktan hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya bayyana babban kalubalen da suke fuskanta dangane da masu dauke da cutar Coronavirus. Jaridar Punch ta ruwaito Dakta Chikwe ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, inda yace matsalar da suke fuskanta shi ne yadda zasu killace mutanen da suka dauke da kwayar cutar, amma babu wata alamar cutar a tattare da su.

A cewar Dakta Chikwe: “Idan har mutum ba shi da wata matsala da ido za ta iya gani, amma kuma yana dauke da kwayar cutar, hakan zai sa ba zai iya zama a dakin da muka killace shi ba, don haka muke basu daman yin amfani da wayoyinsu don tuntubar yan uwa da abokan arziki."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN