Legit Hausa
Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar hana fitar da ya kakabawa al'ummar birnin tarayya Abuja, jihar Legas da Ogun, da tsawon mako daya. Shugaban kasan ya sanar da hakan ne a jawabin da yayi ga yan kasa karo na uku kan lamarin annobar Korona.
Yace:"Dokar hana fita a FCT, Legas da Ogun zai cigaba da kasancewa zuwa ranar 4 ga Mayu, 2020." Amma daga ranar 4 ga Mayu, Buhari ya bayyana cewa za'a fara saukake dokar hana fitar a wadannan garuruwan.
Yace: "Bisa ga shawarwarin da kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19, kwamitocin duba illan lamarin ga tattalin arzikin kasa da kungiyar gwamnonin Najeriya, na bada umurnin saukaka dokar hana fita a FCT, Legas da Ogun fari daga ranar Litnin, 4 ga Mayu, 2020." "Amma za'a yi hakan tare da kara yawan gwaji da bibiyan wadanda sukayi mu'amala da masu cutar."
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari