Al'umman jihar Kebbi sun koma begen tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari

Sakamakon bincike da muka gudanar a Mujallar ISYAKU.COM bisa jita jita da ke zagayawa a cikin al'umma dangane da zabukan 2023, ya nuna fa nan gaba ba wanda jama'a za su saurara kamar Sa'idu Dakin gari domin samun alkiblar siyasa a jihar Kebbi.

Binciken mu ya nuna cewa wannan yana da nasaba ne da gaskiya da ta yi halinta, domin dai jama'a sun gano cewa:
1. Sa'idu ba makaryaci bane
2. Ba maketaci bane
3. Ba masharranci bane
4. Ba dan bakin ciki bane
5 Yana sauraron manya da kanana
6  Yana daukan shawara kuma ya yi amfani da shawaran al'umma
7. Baya kyamar jama'a ko rena hankalin al'umma
8. Yana da kunya da mutunci
9. Ya yi wa kowane bangare na jihar Kebbi adalci a mulkinsa
10. Ta tabbata Sa'idu Dattijo ne.

Wadannan su ne kadan daga cikin sakamakon abin da muka  tattaro daga jama'a dangane da yadda jama'a ke kallon Sa;idu Dakingari a fagen rayuwa da siyasar jihar Kebbi.

SU WAYE DATTIJAN SIYASA A JIHAR KEBBI?

A mataki na manyan 'yan siyasan jihar Kebbi, binciken mu ya nuna cewa Sa'idu Dakingari yana cikin jerin wadanda jama'a ke ma kallon Dattijai masu mutunci, wanda suka hada da :

1.Alhaji Sa'idu Dakingari
2.Alhaji Adamu Aliero
3.Janar Muhammadu (Magoro mai murabus)

Wadannan Dattijai sun tsira da mutuncinsu a idanun al'umman jihar Kebbi, domin rawar mulki da suka taka a zamaninsu rawa ne na mutunci da Dattaku wanda shi ne ke biye da su har yanzu. Kamar yadda Bahaushe ya ce "Wanda ya shuka alhairi, zai girbe alhairi".

MARTABAR SIYASA

Mujallar ISYAKU.COM ya gano cewa tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari ne ya fi kowane Gwamnan jihar Kebbi yin ayyuka ga al'umma bisa tarihi kawo yanzu.

Mun auna wannan ne bisa manyan ayyuka da ke wanzuwa a zahiri a rayuwar al'umma ta yadda tasirin ayyukan da ya yi suka bayyana a kowane sako da lungu na jihar Kebbi.

Wannan ya hada da samar da:

1.Gina filin sauka da tashin jiragen sama na Sir Ahnadu Bello da ke garin Ambursa
2. Samar da Babban Asibiti Kebbi Medical Center KMC a  garin Kalgo
3 Yin hanyoyin mota managarta a kowane Masarauta na jihar Kebbi
4. Samar da Makarantar koyar da fasaha na jiha a garin Dakingari
5. Gina managartan hanyoyin mota da kwalbatoti a agarin Birnin kebbi
6. Ya bayar da mukaman siyasa bil hakki, gaskiya da adalci
7.Ya martaba Sarakunan jihar Kebbi ta hanyar sauraronsu da amfani da shawararsu

ARZIKI YA RATSA AL'UMMA

A zamanin Sa'idu Dakingari, jama'ar jihar Kebbi sun sami wadata, wanda a bayyane yake cewa fiye da rabin gidaje da jama'a suka gina a sabbin unguwannin a garin Birnin kebbi kamar unguwannin Bayan Kara da Filin Sukuwa, duk an gina su ne a zamanin Sa'idu Dakingari sakamakon wadata da al'umma suka samu a zamanin mulkinsa a jihar Kebbi. Haka zalika a garuruwan kananan hukumomi a jihar Kebbi.

JAMA'A NA BEGEN SA'IDU DAKINGARI

Yanzu haka a garin birnin kebbi da kananan hukumomin jihar Kebbi, tsofaffin wakokin siyasa da na rayuwa da Mawaka suka rera wa Sa'idu Dakingari a zamanin mulkinsa  na ci gaba da zagyawa a cikin a;'umma. Lamari da ke bayyana irin tasiri da tsarin rayuwar Sa'idu ke ci gaba da samun gindin zama a zukatan jama'a a jihar Kebbi, wanda masana kan harkokin siyasa suka yi nuni da cewa shakka babu Sa'idu zai zama mai tasairin gaske a fagen siyasan jihar Kebbi sakamakon yadda martaba da mutuncinsa ke kara haskakawa.

KO SA'IDU ZAI SAKE TAKARAR GWAMNA A JIHAR KEBBI?

Bincike da muka gudanar ya nuna cewa tsarin mulkin Najeriya bai bayar da daman takaran kujeran Gwamnan jiha ko na shugaban kasa sau uku ba. Sa'idu ya zama Gwamna a karo na farko na tsawon shekara hudu, ya kuma sake cin zabe ya yi wasu shekaru hudu, jimila shekara takwas kuma karo na biyu kenan. Bisa kundin tsarin mulki na 1999 ba zai sake takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi ba. Amma bisa manuniya na masu fashin baki kan harkar siyasan jihar Kebbi, sun yi amannan cewa Sa'idu zai yi tasirin gaske kan harkokin siyasan jihar Kebbi nan ba da dadewa ba.


Rahotun Isyaku Garba Zuru


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN