Covid-19: Jama'a sun koma amfani da yadi domin dinka abin kariyar fuska

Yayin da ta tabbata cutar coronavirus na kisan bayin Allah a Duniya, wanda ya zama wajibi jama'a su dauki matakin kariya daga kamuwa daga wannan cutar. Yanzu haka a ko'ina a fadin Najeriya, farashin abin kariya da ake sakawa a fuska domin kare baki da hanci ya karu matuka.

Bugu da kari, ga dokar hana fita ko zirga zirga, wanada  ya zama dole jama'a su nema wa kansu mafita. Yanzu haka a birnin Lagos, jama'a sun fara amfani da yadi mai tsabta domin amfani da su wajen rufe baki da hanci. Galibi dai wadannan abin kariya Teloli ne ke dinka su.

Sakamakon haka ake ganin ya kamata jama'a a sauran sassa na Najeriya su yi koyi wajen amfani da Teloli domin su dinka irin wadannan ababen kariya da yadi masu tsabta domin taimakon jama'a.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN