• Labaran yau


  Yadda wasu magidanta makiyaya biyu suka kashe kansu wajen fada domin wata mata

  Wasu makiyayan dabbobi guda biyu sun mutu bayan sun yi wa kansu munanan rauni da adda yayin da suke fada saboda wata mata a Oljorai da ke Gilgil a kasar Kenya.
   
  Wannan lamari ya ba jama'a mamako ganin yadda aka sare wuyar daya daga cikin makiyayan kuma ya mutu nan take, yayin da dayan kuma ya mutu jim kadan bayan an kai shi wani Asibiti.
   
  Wani ganau mai suna Abel Kiprokon ya ce, mutanen biyu suna soyayya da matar ce uwar yara uku, tun shekara biyu da suka gabata ba tare da sun sani ba sai daga bayannan
   
  Mutanen guda biyu basu san junansu ba, sai ranar Laraba lokacin da daya daga cikinsu ya ga dayan yana karyawa da safe a gidan matar.

  Daga bisani rigima ya sa mutanen biyu suka afka wa junansu ta hanyar yin amfani da adda.

  Kwamishinan yankin Gilgil, Ndambuki Mutheki ya ce yansanda na gudanar da bincike kan lamarin, kuma sun kama matar da aka yi rikici a kanta.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda wasu magidanta makiyaya biyu suka kashe kansu wajen fada domin wata mata Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama