Wasu karin mutum 23 sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya bayan adadin farko

Rahotun Legit Hausa

Rahoto da muka samu daga hukumar da ke kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ya nuna cewa an sake samun karin sabbin mutane 23 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce tara daga cikin mutanen sun kasance a jahar Lagas ne, bakwai daga Abuja inda biyar suka fito daga jihar Akwa Ibom sai kuma mutum daya daga jahar Bauchi.

Yanzu haka jumullar mutane da ke dauke da cutar a kasar sun zama 174, an salami mutane tara yayinda biyu suka mutu. A gefe daya mun ji cewa wani direban motan haya da ya kamu da cutar Coronavirus ya gudu daga inda aka killaceshi a garin Bida, jihar Neja kuma na bazama nemansa yanzu.

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Mohammed Makunsidi, ya alanta nemansa ruwa a jallo kuma gwamnati ta nada kwamiti na musamman domin nemoshi. Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a Minna, Makunsidi yace: "Mun yi mamakin guduwarsa kuma yadda ya gudu daga asibitin abin mamaki ne garemu har yanzu amma an harzuka wajen kamoshi."

"Mun samu labarin cewa ya gudu cikin Bida, kuma muna biye da shi yanzu. Mambobin hukumar yaki da COVID-19 da jami'an ma'aikatar lafiya na Bida yanzu domin nemansa da kuma tabbatar da cewa ya yi abinda cibiyar NCDC ta umurcesa."

Kwamishanan ya kara da cewa an killace wasu mutane biyu da suka dawo daga kasar Birtaniya da Canada a garin Kontagora kuma ana gwada su.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN