• Labaran yau


  Yadda gajimari suka hada siffa mai ban al'ajabi a sararin samaniya

  Hoton gajimari da aka dauka da dare ranar 12 ga watan Aprilu a birnin Ikko watau Lagos, ya nuna yadda gajimari suka fitar da wani siffa mai ban al'ajabi da ya yi kama da fuskar dan Adam a sararin samaniya.

  Wata mazauni Lagos Ijeoma Onuoha, wacce ta dauki hoton, ta ruwaito cewa " Idan kana cikin daki, ka fito yanzunnan ka kalli sararin samaniya, wannan abin yana faruwa yanzu, lalle Duniya ta zo karshe".

  Sau da yawa akan sami yanayi da gajimari ke haduwa su bayar da wata siffa da ta yi kama da wata dabba, bil'adama ko wani abu da ke jan hankalin jama'a da al'ajabi.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda gajimari suka hada siffa mai ban al'ajabi a sararin samaniya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama