Basaraken kasar Thailand Maha Vajiralongkorn mai shekara 67, wanda aka fi sani da suna Rama X, ya karya dokar hana fita bayan ya fito daga wajen da ya killace kanshi tare da 'yan mata 20 a kasar Jamus, kuma ya tafi kasar Thailand domin halartar biki a birnin Bangkok.
Basaraken ya yi tafiyar mil 12,000 cikin awa 24 inda ya bi ta birnin Zurich na kasar Switzerland ya dauki uwargidansa Gimbiya Suthida wacce ta killace kanta a gida.
Basaraken ya je kasar Thailand ya halarci bikin al'adar gidan Sarautar kakanninsa wanda ya samo asali tun karni na 1782.
Daga bisani basaraken ya koma wajen da ya killace kanshi a Otel na The Grand Hotel Sonnenbichl da ke Garmisch-Partenkirchen a kasar ta Jamus.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari