Dokar hana fita: Yan fashi sun fara kai farmaki gida-gida tare da tayar da hakali a Lagos

Rahotun Legit Hausa

An shiga tashin hankali a yankunan Mangoro, Ogba, Agege, Iyana Ipaja da kuma Dopemu da ke jahar Lagas, yayinda yan ta’adda suka yiwa mazauna yankunan fashi da makami.

A wani lamari mai kama da shiryayyen aiki, an tattaro cewa yan fashin sun isa yankunan a kan babura da manyan motocin bas, dauke da makamai daban-daban.

Mazauna yankunan sun bayyana cewa barayin sun sace kayayyakin abinci a shaguna da manyan dakunan ajiya da ke yankunan, jaridar TheCable ta ruwaito. “Sun zo da misalin karfe 7:00 na dare da babura guda 30 da manyan motocin bas guda 10,” in ji wani mazaunin Aluminium Village a Dopemu.

“An yiwa gidaje da dama da shagunan siyar da kayan abinci fashi. Sun ma fasa wasu manyan dakunan ajiya sannan suka sace kayayyakin da ke wajen.” A yankin Mangoro, wani mazaunin wajen ya bayyana cewa mutane na unguwanni, suna yiwa mutane kwace

A Iyana Ipaja, wani mazaunin wajen ya ce bayan hare-haren da aka kai, wasu matasa a yankin sun cinnawa tayoyi wuta a unguwanni. A wani sako da aka wallafa a soshiyal midiya, wata mazauniyar Agege ya ce: “A yanzu bamu tsira ba a Agege.

Daga Oko koto, Agunbiade, Ayanwale zuwa Pen Cinema. Muna bukatar taimako; mun kira yan sanda amma babu amsa,” in ji ta. “Kusan awa daya da ya gabata, babu wanda ya kawo mana agaji. Wacce irin kasa ce wannan? "Sun killace mu ba tare da kowani tallafi ba. Rayuwarmu n a cikin hatrsari.

Wadannan yaran sun shigo yankinmu. Kusan su 100. Suna ta fashi kusan sama da awa daya.” Bala Elkana, kakakin yan sandan jahar Lagas, ya zargi wadanda suka kona tayoyi da haddasa tashin hankali a yankunan.

“Mun aika jami’anmu wajen, kuma abunda muka lura da matasan shine cewa suna fitowa da sunan kare yankunansu daga yan fashi,” in ji shi. “Sannan suna kona tayoyi da sunan kare kai, alhalin wannan kadai ma yana haifar da tashin hankali ne.

Mun aika wani gagarumin sako, umurnin shine a zauna a gida. "Dole kowa ya zauna a gida. Muna da isassun jami’an tsaro a wannan lokacin. Bama fuskantar kowani barazana. "Wadannan matasan na neman damar da zai sa su fito daga gida ne, don haka suke haddasa tashin hankali.

Akwai isassun yan sanda da ke sintiri a yankunan.” A wani labarin kuma, mun ji cewa wani sabon rikicin kabilanci ya barke a jahar Taraba tsakanin kabilun Shomo da Jole dake karamar hukumar Lau ta jahar. Hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Daily Trust ta ruwaito a sanadiyyar rikicin, an kona garin Shomo Sarki gaba daya, inda a nan ne aka fi samun asarar rayuka da dukiyoyi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN