Ya dawo da mura da zazzabi daga Lagos, jama'an gidansu sun gudu daga gidan a Kaduna

Rahotun Legit Hausa

Wasu mazauna unguwar Kurmi da ke yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun shiga rudani bayan wani matashi da ya dawo daga Legas ya fara nuna alamun masassara.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa jama'ar unguwar sun kara gigita bayan mazauna gidan da matashin yake sun gudu bayan ya fara nuna alamun masassara kwatankwacin ta masu dauke da cutar covid-19 tun bayan dawowarsa daga jihar Legas a ranar 5 ga watan Afrilu.

Liman Hamisu, dagacin garin Kurmin Kaduna, ya shaidawa NAN cewa 'yan uwan mutumin sun tsere daga gidansu bisa tsoron cewar ko ya kamu da kwayar cutar coronavirus. "Mutanen gidan sun gudu sun barshi bayan ya fara amai da zazzabi mai zafi.

"Bayan guduwar mutanen gidan, sai jama'ar unguwa suka shiga halin damuwa bisa tunanin cewa ko ya gudo daga cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da ke Legas," a cewar Hamisu.

A cewarsa, mutanen unguwa sun kira cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) da wakilan jami'an lafiya daga karamar hukumar Igabi, kuma dukkansu sun tabbatar da cewa alamun rashin lafiyarsa ba su yi kama da na mai dauke da cutar covid-19 ba.

"Bayan mun addabi hukumar NCDC da kira, ta turo wakili zuwa garinmu domin ganin halin da ya ke ciki. "Kazalika, wani jami'in hukumar lafiya daga karamar Igabi ya tabbatar da cewa mutumin ba ya dauke da kwayar cutar covid-19," a cewarsa.

Dagachin ya roki 'yan uwan mutanen da su daure su dawo gida don yanzu an tabbatar da cewa dan uwansu ba ya dauke da kwayar cutar covid-19 domin dawowarsu ce kadai za ta kwantar da hankalin mutanen unguwa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN