An shawo kan cutar coronavirus a birnin Wuhan, an dage dokar hana fita daga gida - Hotuna

An dage dokar hana fita a birnin Wuhan, birni da cutar coronavirus ta samo asali a kasar China. An dage dokar ne bayan mako 10 da ayyanawa saboda hana cinkoson jama'a.

An hana zirga zirga tare da hana jama'a fitowa daga gida a birni da ke da yawan jama'a miliyan 11 tun ranar 23 ga watan Janairu, babu shiga ko fita daga birnin bayan an tabbatar da mutum 82,000 sun kamu da cutar yayin da mutum 3,331 suka mutu.

Daga karshe dai mahukunta sun ce an shawo kan kwayar cutar, sakamakon haka aka dage dokar hana fita.

Hotuna da aka dauka a birnin ranar Laraba 8 ga watan Aprilu, ya nuna yadda jama'a suka dinga fitowa daga gidajensu suna zuwa wajen aiki tare da hada hada.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN