Shugaban kungiyar, Malam Habibu Bello, ya yi jawabi kan tsarin ayyukan taimaka wa matasa da Abubakar Malami ke yi wa jama'a, manufofinsa na alkhairi, tsare tsaren kawo ci gaba da wadata ga matasa da sauran shir ye shiryen alkhairi da Ministan ya sa gaba domin jama'ar jihar Kebbi.
Malam Habibu, ya shaidamana cewa, " Mun shirya wannan taron ne domin ci gaba da wayar wa matasa kai dangane da ayyukan alkhairi da maufofin Abubakar Malami (Chika)".
Ya kuma kara da cewa " Wasu matasa sun ce sun bar siyasa gaba daya, amma saboda soyayyarsu da mu, sun ce za su mara masa baya".
"Saboda haka zamu sake yin irin wannan taro a nan Badariya ranar 24 ga watan Afrilu 2020".
Wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da
Malami Malas Jodu- wanda ke kula da unguwar mai Rago, da unguwar Dambo.
Sai Abubakar Jatau ,wanda ke kula da Kola, Tarasa da Badariya.
Sauran sun hada da Ahmed Hali da Mika'ilu Bello.
Karkashin shugaban Mata kuwa akwai, Malama Samira Badariya, Fatima Abubakar Badariya da Shamsiya Muhammed.
Rahotun Isyaku Garba Zuru
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari