• Labaran yau


  Coronavirus: Gwamnati ta fara raba wa talakawa kudi kyauta

  Rahotun Jaridar Aminiya

  Gwamnatin Najeriya ta fara raba wa marasa galihu da ke Yankin Babban Birnin Tarayya N20,000 ko wanne don rage masu radadin dokar da aka ayyana ta hana fita a yankin.

  Wadanda za su ci moriyar tallafin dai marasa galihu ne a yankin su 50,000 wadanda ke karkashin tsarin gwamnati na bayar da N5,000 duk wata bisa sharadi.

  A jawabin da ya yi ranar Lahadi na ayyana dokar ta hana fita, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya bayar da umarni a bai wa wadannan mutane kudin su har na watanni biyu nan take.

  Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwato Ministar Ayyukan Jinkai da Agajin Gaggawa Hajiya Sadiya Umar yayin kaddamar da aikin a karamar hukumar Kwali tana cewa matakin bin umarnin shugaban kasa ne.

  “Naira 5,000 ake bai wa masu cin gajiyar wannan tsari duk wata; don haka N20,000 din da za a bai wa ko wanne yanzu na wata hudu ke nan.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Coronavirus: Gwamnati ta fara raba wa talakawa kudi kyauta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama