Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da mutuwar mutum daya sakamakon cutar coronavirus a jihar.
Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Masarin ne ya sanar da manema labarai haka. Ya ce wani Likita wanda ke zaune a garin Daura mai zaman kansa mai suna Dr. Aminu Yakubu, ya dawo daga Lagos sai ya rasu bayan kwanaki uku da dawowarsa.
Ya ce an kai samfur na jininsa NCDC a birnin Abuja domin gwaji, daga bisani sakamakon gwaji da aka yi masa ya nuna yana dauke da cutar coronavirus.
Gwamna Masari ya ci gaba da cewa Dr Yakubu dan asalin jihar Kogi ne, kuma yana fama da cutar hawan jini da ciwon suga kafin ya kamu da cutar coronavirus wanda ake kyautata zaton cewa ya kamu da cutar ne lokacin da ya je Lagos
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari