Dokar coronavirus: Duba abin da ya faru da 'yan mata 30 a hannun 'yansanda

Jama'ar kasar Uganda  sun wayi gari ranar Asabar 4 ga watan Aprilu da labarin yadda ake zargin jami'an tsaro sun likida wa 'yan mata 30 tare da wasu maza dukan tsiya, kuma suka mulmula su a cikin cabo yayin tabbatatr  da dokar hana fita musamman da  dare sakamakon cutar coronavirus.

Wannan lamari ya faru ne a garin Eleguda da ke bakin iyaka tsakanin kasar ta Uganda da Sudan.

Tun ranar 30 ga watan Maris, shugaba Museveni ya ayyana dokar hana fitan dare sakamakon cutar coronavirus.

Sai dai jama'a na zargin jami'an tsaro tare da hukumar leken asiri da 'yan sa kai, suna dukan mutane tare da wulakanta su da sunan tabbatar da dokar coronavirus.

Wata majiya ta ce jami'an tsaron sun yi zargin cewa mata da aka kama karuwai ne da suka ki bin umarni.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN