Duba dalili da ya sa wasu mutane ke warke cutar coronavirus da gaggawa

Rahotun Legit Hausa

Shugaban likitoci na asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan, Farfesa Jesse Otegbayo, ya bayyana dalilin da yasa mutane ke warkewa daga cutar coronavirus cikin kwanaki kalilan. A yayin jaddada wannan ci gaban, ya ce mutane bai kamata su dinga mamakin hakan ba.

Otegbayo ya ce akwai wasu abubuwan da suka hada da tsohuwa cuta, karfin garkuwar jiki da kuma kwayar cuta jiki yana tantance kwanakin da kwayar cutar ke yi a jiki. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da jaridar The Nation a kan yadda killace kai ke faruwa. Shugaban asibitin dai a makon da ya gabata ne ya bayyana baya dauke da cutar bayan a ya dau kwanaki takwas yana jinyar cutar.

Shugaban asibitin ya yi bayanin cewa kwayar cutar ya fi illata masu tsohuwar cuta irinsu daji, ciwon zuciya, ciwon sukari da sauransu. Ya kara da cewa masu garkuwar jiki mara karfi sun fi fuskantar matsala babba idan kwayar cutar ta shiga jikinsu.

Ya ce: "Warkewar da nayi daga cutar cikin kwanaki kalilan ya faru ne sakamakon garkuwar jiki na. Wasu garkuwar jikinsu bata da karfi. A misali, idan mutum na yin mura kuma yana tari, wasu mutane na iya yin mu'amala dasu ba tare da sun kwashi cutar ba.

Wasu kuwa babu dadewa suke dibar cutar." Ya kara da cewa, "masu ciwuka da ke nan a jikinsu na iya faduwa saboda kwayar cutar. Idan mutum yana dauke da cutar daji, ciwon zuciya ko kuma ciwon sikafi, akwai yuwuwar garkuwar jikinsu ta zama mara karfi." Otegbaya ya ce, bai dace mutanen da suka warke daga cutar ba su koma aiki da gaggawa ko kuma su fara mu'amala da jama'a ba.

Hakan yana daga cikin abubuwan da cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta sanar. "Ga wadanda suka warke daga cutar, ya kamata su gaggauta bin dokokin NCDC. Bayan gwaji na biyu, ana zaunawa a gida ne ba tare da an je aiki ba na kwanaki bakwai. Duk wadanda suka karya wannan dokar na karya dokokin kiwon lafiya ne," in ji shi.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN