Abin
al'ajabi baya karewa a wannan Duniya, duba da cewa Mahaifiya ce aka fi
sani da tausayin diya ko da da ta haifa. Amma ba haka lamarin yake ba a
wata mata. Domin dai wannan matar ta bizine jaririn da ta haifa ne da
ransa kuma da hannunta.
Dubun wannan matar ta cika ne
bayan matasan gari sun daina ganinta goye da danta, sakamakon haka suka
tuhume ta, daga bisani dai ta ce ta bizine jaririn ne a daji, kuma ta
kai matasan wajenda ta bizine jaririn da ransa. Amma ko da aka tone
jaririn ya riga ya mutu, duba da cewa yana abinne da ransa har tsawon
yan kwanaki.
Ba a fayyace takamammen wajenda lamarin ya faru ba a rahotu da muka samu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari