Shekara daya da rasa Dattijon amana Alh Lawal Kawara a unguwar Nassarawa 2 B/kebbi

Yan kwanaki da suka gabata, a wannan wata na Aprilu, Marigayi Alhaji Lawal Kawara ya cika shekara daya da rasuwa bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya. Margayin ya sami kyakkyawar karshe, da kuma kyakkyawar Jana'iza da ya sami halartar dimbin jama'a daga ciki da wajen garin Birnin kebbi.

Marigayi Alhaji Lawal Kawara ya yi rayuwarsa ne, kuma Allah ya karbi ransa a ranar  27 ga watan Aprilu na shekara 2019 a garin Birnin kebbi. Gidansa na karshen layin gidan Marigayi Umaru Gwandu,a unguwar Nassarawa 2 Birnin kebbi.

AN RASA DATTIJON AMANA

Bayan rasuwar Alhaji Lawal Kawara, a zamantakewa na yau da kullum, sai gaskiya ta yi halinta, domin ta bayyana kuma tabbace, cewa ashe duk wani zumunta da aka dage da sadarwa, Marigayin ne ke tafiyar da shi a cikin unguwan.

Ta tabbata cewa Marigayin ne yake aikawa kowane gida domin a sanar da  makwabta ko da akwai wani lalura ko sha'ani. Yakan aika wasu Dattijai domin su sanar da kowane makwabci idan akwai wani lamari.

Amma bayan rasuwarsa, sai aka gano cewa ashe wannan bawan Allah ne ke tafiyar da wannan kyakkyawar tsari na zamantakewan makwabtaka.

ABIN DA YA DAMEKA YA DEMESHI

Duk wata lalura da ta sami makwabci, lallai ta shafi Marigayi Alhaji Lawal, domin yakan yi dumu dumu wajen ganin lalurar makwabci ya kau, ko an magance shi bisa mutunci da adalci kuma bil hakki da gaskiya.

Dattijo ne da zai iya baka abinshi ko da yana so idan makwabci ya nuna kauna ga wannan abin. Wanna ya bayyana a zahiri bayan rasuwar Alhaji Lawal.

YA WADATU DA RAYUWA

Marigayi Alhaji Lawal mutum ne mai hakuri tare da wadatar zuciya. Baya cikin irin mutane da ke da manufar idan na samu makwabci ma ya rasa ban damu ba. Dattijo ne mai kyakkyawar zuciya wacce ke cike da tsabta, wadata, kauna tare da mutunta makwabci bisa tsarin zumunci da adalci.

Dattijo ne da ke bin makwabta da alheri, kyauta da zumunta, baya kuma bukatar ya yi babakere domin ya tilasta makwabci neman wani abu a wajensa domin neman girma.

AN RASA WANDA YA MAYE GURBINSA

An rasa gurbin halaye irin na Marigayi Alhaji Lawal Kawara. Bayan rasuwarsa a wannan unguwa, ababe da yawa na zumunci ba tare da nuna bangaranci, kabilanci ko gazawa ba ya yi karanci. A zamaninsa, babu yadda za a yi a aiwatar da wani abu ba face an tabbatar cewa kowane magidanci kuma makwabci yana ciki.

Idan makwabci ya yi kasa a guiwa kan lamarin, idan har lamarin na jama'ar unguwa ne, Marigayi Alhaji Lawal zai tabbata cewa ya je gidan wannan makwabci da kanshi, duk da tsufarsa, domin  ya bincika ko lafiya wannan makwabci bai sa kansa a wannan harka na jama'ar unguwa ba.

Idan kuma abin da zai iya taimakawa ne  domin ganin wannan magidanci ya sami taka rawa a wannan lamari, Marigayi Alh. Lawal zai yi ruwa da tsaki, wani lokaci har ma zai yi amfani da kudinsa domin ganin an yi nassara a kan wannan tsari.

KYAKKYAWAR KARSHE

Duniya da makwabta sun tabbatar cewa Alhaji Lawal Kawara Dattijon amana ne mai mutuncin gaske wandazuciyarsa ke cike da adalci, tausayi, mutunci da kaunar makwabta, ba tare da laakari da ko wane bangare na Najeriya suka fito ba.

Duniya da makwabta za su yi maka kyakkyawar shaida a Duniya da Lahira bisa kyakkyawar zuciya da halayenka.

Allah ya jikanka ya yi maka gafara Baba.

Rahotun Isyaku Garba Zuru

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN