Mahukunta a jihar Kano sun kama wani matashi mai suna Mubarak Bala bayan an shigar da kara a kansa a Shelkwatan yansandan jihar Kano bisa zargin cin zarafin Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW)
Wani ofishin Lauyoyi a jihar Kano ne ya shigar da karar Mubarak Bala wanda ke zaune a layin Masallaci Bilal a rukunin gidaje na Karkasawa a birnin Kano, bayan ya wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook wanda Lauyoyin ke ganin cewa cin zarafin Manzon tsira ne kuma yunkuri na harzuka al'umma Musulmi domin su tunzura su daui doka a hannunsu.
Mubarak ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa " Babu banbanci tsakanin Annabi TB Joshua (S.A.W) da Muhammadu (A,S) na Saudiyya, gara ma namu na Najeriya bay ta'addanci".
Wadannan kalamai tuni suka ja kace nace a shafukan sada zumunta a Arewacin Najeriya.

https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari