Rahotun Legit Hausa
Gwamnan
jihar Kaduna Nasir Elrufa'i ya ce sun samu karin mutum 19 masu dauke da
cutar korona, al'amarin da ya kara yawan adadin masu cutar a jihar daga
9 zuwa 25.
Elrufa'i
wanda ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Twitter ya ce an yi wa
almajiran guda 40 gwaji inda sakamakon 19 daga cikinsu ya nuna suna
dauke da cutar ta korona.
Gwamna
Elrufa'i ya kuma kara da cewa yanzu ta tabbata shigi da fici da ake yi
wa jihar tasa ne ke janyo karuwa masu cutar a Kaduna, inda ya ja
hankalin jami'an tsaro da su ci gaba da sanya ido kan duk masu shiga
birnin ta barauniyar hanya.
Ko
a makon da ya gabata ma sai da gwamnan ya sanar cewa sun samu biyar
daga cikin almajiran da aka mayar wa jihar tasa daga Kano masu dauke da
cutar.
A
kokarin dakile bazuwar cutar korona a birnin Kano ne dai ya sa gwamna
Abdullahi Umar Ganduje ya fito da shirin mayar da almajirai jihohinsu na
asali.
Da dama masana harkar lafiya sun soki shirin bisa dogaro da cewa hakan ka iya fantsama cutar a wasu jihohin da ba su da ita.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari