Rahotun BBC Hausa
An
ci gaba da arangama cikin dare na biyu tsakanin jami'an tsaro da masu
zanga-zanga a Tripoli, birni na biyu mafi girma a Lebanon.
Masu zanga-zanga sun cinna wuta kan bankuna bayan jana'izar wani takwaransu dan shekara 26, da ya mutu sakamakon harbin bindiga.
'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar da ke jifa da duwatsu.
Matakan
kulle saboda annobar korona sun kara ta'azzara matsalolin tattalin
arziki a Lebanon, inda farashi ke hauhuwa kuma darajar kudin kasar ke ci
gaba da faduwa kasa warwas.
Shugaba
Yoweri Museveni na Uganda ya bullo da sabbin matakan dakile yada cutar
korona ta hanyar direbobin motocin daukar kaya bayan gwaji ya nuna cewa
wasu fiye da 20 da suka shiga kasar daga Kenya na dauke da cutar.
Ba za a bar direbobi su rika daukar fasinjoji ba ko su kwana a otel ko gidajen wasu mutane.
Gwajin cutar ta korona ala tilas tuni ya haddasa cunkoson dumbin ababen hawa a kan iyaka tsakanin Kenya da Uganda.
An
dai ce direbobin motocin daukar kaya da yaransu a Kenya kan sha zaman
jiran dogon layi tsawon kwanaki don yi musu gwajin korona kafin a bari
su tsallaka zuwa Uganda.
Hanyar
Mombasa mai tashar jirgin ruwa a Kenya, muhimmiya ce ga sufurin abinci,
magunguna da sauran kayan tilashin rayuwa zuwa Uganda da Rwanda da
Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.
Sabbin
alkaluma sun nuna cewa annobar korona ta kashe Amurkawa fiye da yakin
Biyatnam. Alkaluman dai sun nuna cutar ta kashe Amurkawa sama da dubu
58, kuma ta harbi fiye da mutum miliyan daya a kasar, kusan kashi daya
cikin uku na daukacin adadin mutanen da suka kamu da cutar a fadin
duniya.
Bayanan sun zo ne daga Jami'ar Johns Hopkins, amma ana jin cewa lissafin ya gaza ainihin yadda lamarin yake.
Da
aka tambaye shi kan miliyan daya na yawan masu cutar da Amurka ta
cimma, Shugaba Trump ya ce hakan ta faru ne saboda Amurka ta gudanar da
gwaji mai yawan gaske.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari