• Labaran yau


  Jamus ta ba Najeriya Naira biliyan 2.2 don taimakon jama'an Yobe,Adamawa da Borno

  Gwamnatin kasar Germany watau Jamus ta ba Najeriya kyautar karin  €5.5 million daidai da Naira biliyan 2.2bn kudin Najeriya, domin ceton rayukan jama'an jihohin Yobe, Borno da Adamawa sakamakon cutar coronavirus.

  Sanarwar haka ta fito ne daga shafin Twitter na ofishin jakadancin kasar Jamus da ke Najeriya.

  Wannan ya kawo yawan adadin taimakon kudi da kasar Jamus ta ba Najeriya ta hannun ofishin jinkai jama'a na kasa zuwa  Euro Miliyan €29 tun likacin da ta fara aikinta a 2017 wanda ya sa Jamus ta zama kasa da ta fi bayar da taimako mafi yawa.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jamus ta ba Najeriya Naira biliyan 2.2 don taimakon jama'an Yobe,Adamawa da Borno Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama