Mutum 6 masu cutar coronavirus sun tsere daga inda aka killace su a jihar Osun

Jaridar Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamnatin jihar Osun ta alanta neman mutane shida masu cutar Coronavirus ruwa a jallo bayan sun gudu daga inda aka killacesu a Ejigbo, jihar Osun ranar Juma'a.

Mutanen na cikin tawagar matafiyan da suke shigo Najeriya daga kasar Cote d'ivoire a makon da ya gabata kuma aka samesu da cutar ta COVID-19.

A lokacin gwamnatin jihar ta killacesu a kauyen Ejigbo. Wani jawabi daga gwamnatin jihar ya bayyana sunayen mutane shidan da lambar wayarsu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post