• Labaran yau


  Zargin cin zarafin budurwa: Gwamna Yahaya Bello ya dakatar da kwamishinansa

  Gwamna Yahaya Bello ya bayar da umarnin dakatar da Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kogi Mr Abdulmumini Danga wanda ake tuhuma da yi wa wata budurwa fyade tare da dukanta.

  Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar Kogi ta ce Gwamna Bello ya bukaci 'yansanda sun hanzarta gudanar da bincike da suke yi kan lamarin.

  Idan baku manta ba, mun labarta maku cewa wata yarinya mai sun Elizabeth Oyeniyi ce ta fallasa abin da ta yi zargin cewa Kwamishinan ya yi mata fyade kuma ya yi mata duka bayan ta wallafa rubutu dangane da Kwamishinan a shafinta na Facebook.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zargin cin zarafin budurwa: Gwamna Yahaya Bello ya dakatar da kwamishinansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama