An gudanar da Sallar Juma'a a mafi yawan Masallatan Juma'a a Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi ranar Juma'a.
Sai dai wani ma'aikacin lafiya da baya son a ambaci sunansa ya shaida mana cewa " Kun gan jama'a sun hadu domin yin ibada, amma ku duba da kyau ku gani, jama'a basu yi amfani da abin rufe hanci da baki ba domin ya yi tsada a halin yanzu ana sayar da shi N500 marmakin N20 a baya.
"Idan da Gwam,nati za ta taimaka ta saye su da dama ta ba 'yan agaji su tsaya a bakin kofar shiga Masallatan Juma'a su ba jama'a idan za su shiga Masallaci da sun taimaka kwarai".
Mahukunta a jihar Kebbi sun ce babu wanda aka samu da wannan cuta a fadin jihar, sai dai hukuma na ci gaba da aiwatar da matakan kariya a kan kamuwa da cutar.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari